Mumini ba ya taba mika wuya ga wulakanci
IQNBA - Kada mumini ya karbi wulakanci ta kowace fuska. Ka ga Imam Hussaini (AS) ya ce: Ba mu yarda da kaskanci; Dole ne mu ki yarda da wulakanci har abada. Mumini ba ya karbar wulakanci da kaskantar da kai ga kafirai da kuma mika wuya ga matsin lambar kafirai. [ Jagoran juyin juya halin Musulunci, 23/08/1983].