IQNA

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi salla ga gawar shahid Ismail Haniyyah

15:05 - August 01, 2024
Lambar Labari: 3491617
IQNA - A safiyar yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi sallah  ga gawar shahid Isma'il Haniyyah shugaban kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas tare da halartar al'ummar Tehran da jami'an soji da na kasa da kuma gungun kwamandojin kasar.

A safiyar yau Alhamis 1 ga watan Agustan shekara ta 2024  daidai da 26 ga watan Muharram shekara ta 1446, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci sallar janazar shahid Isma'il Haniyyah shugaban kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a jami'ar Tehran, tare da halartar dimbin al'ummar birnin Tehran

Bayan kammala sallar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya zo wajen gawar wannan shahidi ya yi bankwana da shi ta hanyar karanta Fatiha, sannan aka raka  gawar shahid Isma'il Haniyyah a hannun dimbin jama'a.

Idan ba a manta ba a safiyar ranar Laraba ne  aka kai hari a masaukin  Shahid Isma'il Haniyyah a birnin Tehran, kuma a sakamakon wannan lamari ya yi shahada shi da wani mai tsaron lafiyarsa.

 

 

4229480

 

 

captcha