IQNA

Wasu ‘Yan majalisar Dokokin Burtaniya Sun Soki Gwamnati Kan Batun Nuna Kyamar Musulmi A Kasar

13:17 - August 08, 2024
Lambar Labari: 3491658
IQNA - Mambobin majalisar dokokin Birtaniyya sun soki yadda gwamnatin kasar ta gaza wajen tunkarar kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke kai hare-hare a wuraren musulmi ta hanyar yada kiyayya ga musulmi.

A rahoton Yeni Shafaq, 'yan majalisar dokokin Burtaniya da dama sun soki yadda gwamnatin kasar ke nuna halin ko in kula dangane da tarzomar kyamar musulmi.

Jeremy Corbyn, tsohon shugaban jam'iyyar Labour ta Biritaniya, da wasu 'yan majalisa hudu masu zaman kansu, sun ce abin damuwa ne yadda gwamnati ba ta da wani shiri na ganawa da jami'an Majalisar Musulmi ta Birtaniyya, a daidai lokacin da gungun masu nuna wariya ke kai hari kan masallatai da cibiyoyin 'yan gudun hijira.

Sun caccaki Fira Minista Keir Starmer bisa rashin daukar matakai na tunkarar tarzomar masu tsatsauran ra'ayi a baya-bayan nan, suna masu zargin gwamnatin kasar da gazawa wajen magance kyamar baki da musulmi da ke kara ruruwa a cikin kasar.

A cikin wata wasika, 'yan majalisar sun bayyana rashin jin dadinsu da martanin da Mr Starmer ya mayar ga masu zanga-zangar masu ra'ayin mazan jiya da suka tayar da tarzoma a garuruwan Burtaniya a karshen makon da ya gabata. Sun ce gwamnati ba ta yin abin da ya dace wajen magance abubuwan da suke jawo kiyayya da ke haddasa tashe tashen hankula ba.

A cikin wasikar da suka rubuta wa Yvette Cooper, sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya, wadannan wakilan sun soki lamirin gwamnatin kasar da kuma matsayar da ta dauka da bai dace ba, da kuma rashin sanin muhimmiyar rawar da masu kyamar baki da musulmi suka taka, wajen tayar da wannan tarzoma.

Wadannan 'yan majalisar sun jaddada cewa ambaton abubuwan da za a iya fahimta a cikin maganganun gwamnati za a iya fassara su a matsayin goyon baya ga masu tayar da hankali da rarraba kan al'ummar Burtaniya.

Sun bayyana damuwarsu ta musamman kan matakin da gwamnati ta dauka na kin yin hulda da majalisar musulmi, babbar kungiyar musulmi ta Biritaniya.

Wasikar ta ce: "A daidai lokacin da gungun 'yan daba masu akidar nuna wariya ke kai hare-hare kan masallatai da cibiyoyin 'yan gudun hijira, abin damuwa ne yadda gwamnati ba ta da shirin ganawa da majalisar musulmin Birtaniya. Mun yi imanin cewa, irin  wannan yanayin  ba ya faruwa ga wakilan sauran al'ummomi da addinai a Burtaniya, wanda kuma kamata hakan ta rika faruwa kan mabiya addinin muslunci ba..

'Yan majalisar masu zaman kansu sun yi tir da kalaman da ke alakanta masu neman mafaka da kuma al'ummomi bakia  akasar da cewa su ne ummul haba'isin dukkanin matysaloli zamantakewa da tabarbarewar tatatlin arzikin kasar, da kuma rashin ayyukan yi.

A cikin wasiƙar tasu, Corbyn da abokan aikinsa, sun yi kira da a gudanar da taron gaggawa tare da Cooper don tattaunawa kan matakan da suka dace na yaƙi da ta'addanci da kuma nuna wariya.

Sun yi imanin cewa yanayin siyasar da ake ciki a yanzu ne a kasar Burtaniya ya haifar da wannan tashin hankali. Sun kuma bukaci gwamnati da ta tsaya tsayin daka wajen yaki da kyamar Musulunci da ke haifar da tashin hankali, tare da tallafawa wadanda abin ya shafa.

 

 

 

 

 

4230416

 

 

captcha