Wadanda suka yi fice wajen kisan dan adam
Gwamnatin Sahayoniya ta bar wani sabon ma'auni a tarihin laifukan dan Adam a duniya na ta'addanci, zalunci, da kuma laifuka masu ban mamaki; A yau, ana jefa bama-bamai masu tsanani na sahyoniyawan a kan wadanda ko harsashi ba su da shi; Yara masu shekaru biyar, yara masu shekaru shida, mata, marasa lafiya na asibiti; Ba su yi harbi ko daya a kan kowa ba... Wannan laifi laifi ne da ba a taba yin irinsa ba. [jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran; 26/7/2024]