Zakarar gasar Olympics ta kasar Holand, ta je filin wasa ne sanye da hijabi a lokacin da ta yi nasara tare da lashe lambar zinare a tseren gudun fanfalaki a ranar karshe ta gasar Olympics ta birnin Paris.
Da aka yi nazarin hotunan wannan ‘yar wasa ‘yar asalin kasar Habasha a shafin Instagram, ta bayyana cewa ba ta cikin 'yan wasan da suka sala lullubi kuma ta halarci gasar ba tare da lullubi ba. Sai dai ta sanya hijabi a lokacin da ta karbi lambar yabo ta nuna rashin amincewarta da manufofin kin jini da ake nuna wa 'yan wasa musulmi mata.
Masu fafutuka a shafukan sada zumunta sun sanar da cewa, Sifan Hassan ta yi niyyar aikewa da sako ga masu hana mata saka lullubi, kuma ta yi nasarar zama wata alama a ranar karshe ta karbar lambar zinare da aka raba a gasar Olympics.
Bayan lashe zinare a tseren mita 5,000 da 10,000 da tagulla a tseren mita 1,500 a Tokyo sannan ta samu tagulla a tseren mita 5,10,000 a birnin Paris, wannan 'yar kasar Holland ta kawo adadin lambobin yabo na Olympics guda 6.