Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Kefil ya bayar da rahoton cewa, sashen da ke kula da kayan tarihi na al-Kefil da ke cikin haramin Abbasi ya yi shiri na karshe na kaddamar da ayyukansa a madadin wannan hubbaren a tarukan Arbaeen na Imam Hussain (AS).
Manufar wannan shiri dai ita ce kara wayar da kan jama'a a bangarori daban-daban na al'adu da ilimi, wanda hubbaren ke aiwatarwa ta hanyar ayyuka daban-daban kamar shirye-shiryen kur'ani, tarurrukan al'adu da laccoci na addini, baje kolin littafai, aikace-aikacen dijital, da tuntubar ilimi.
Da yake magana game da shigar da sashen adana kayan tarihi na Al-Kafil a cikin wannan aiki, Sadegh Yazul-Zaidi, shugaban sashen kayan tarihi na Al-Kafil ya ce: "cibiyar kayan tarihi ta Al-Kafil wani bangare ne na jerin ayyukan al'adu a kan hanyar Najaf zuwa Karbala, wanda aka tanada domin masu ziyarar Arba'in Hosseini da ke kunshe da kwafi na abubuwa masu daraja .