A cewar kafar yada labaran Vatican, Paparoma Francis shugaban mabiya darikar katolika na duniya, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai bayan tafiyarsa ta kwanaki 12 a kudu maso gabashin Asiya da Oceania cewa, yana tattaunawa ta wayar tarho da mabiya darikar Katolika na yankin zirin Gaza a kowace rana.
Ya kara da cewa: Idan ka ga gawarwakin yara, idan ka ga ana jefa bama-bamai a wata makaranta bisa zargin akwai wasu dakarun sa-kai, wannan mummunan aiki ne.
Shugaban ’yan Katolika na duniya ya ce: “A wasu lokatai ina tunanin cewa wannan yaƙin ya wuce gona da iri, ina baƙin ciki da in faɗi haka.” Amma ba na jin za su dauki matakin samar da zaman lafiya.
Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya a baya ya yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa, da sakin fursunoni da kuma agajin jin kai ga Gaza ya kuma ce: Cututtuka da dama da suka hada da cutar shan inna na yaduwa a Gaza.
Yayin da yake jaddada cewa Kudus ya zama wurin zaman tare da kiristoci da Yahudawa da Musulmai da kuma karbuwa, ya ce: A zauna lafiya a kasa mai tsarki.
Bayanin na Paparoma na zuwa ne a daidai lokacin da babban jami'in harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrell a ranar Juma'a ya yi kira da a dauki matakin bai daya domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.