IQNA

A ranar Juma'a ne za a yi jana'izar Shahid Nasrallah

16:00 - October 03, 2024
Lambar Labari: 3491972
IQNA – Za a yi taron jana'izar Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a ranar Juma'a.
A ranar Juma'a ne za a yi jana'izar Shahid Nasrallah

Shafin yada labarai na Sabrin ya wallafa wannan labari da safiyar yau (Alhamis) inda ya nakalto  daga wata majiya mai tushe.

Wannan kafar yada labarai ba ta fitar da karin bayani kan lokaci da wurin da aka binne gawar babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da ya yi shahada ba.

Ya zuwa yanzu, babu wani labari ko sanarwa game da hakan da kafafen yada labarai na Lebanon da hukumomin wannan kasa suka buga.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne firaministan gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila  Benjamin Netanyahu tare da goyon bayan Amurka ya bayar da umarnin kashe babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrallah daga hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a New York.

Sakamakon wannan odar, a yammacin ranar Juma'a jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan sun yi ruwan bama-bamai a yankunan mazauna unguwar ​​Harik da ke birnin Beirut. Wasu majiyoyin gwamnatin yahudawan sahyuniya sun sanar da cewa.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta tabbatar da shahadar wannan babban mujahid na kasar Labanon a cikin wata sanarwa da ta fitar a Asabar. Sayyid Hasan Nasrallah ya yi shahada yana da shekaru 64 da haihuwa kuma bayan shekaru talatin da biyu yana matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon.

 

 

4240375

 

 

captcha