IQNA

Mayakan Hizbullah sun hakala tare da jikkata sojojin yahudawa kimanin 80

16:11 - October 03, 2024
Lambar Labari: 3491973
IQNA - Kakakin rundunar yahudawan sahyoniya ya yarda cewa an kashe sojoji takwas na wannan haramtacciyar gwamnati a wani artabu da mayakan Hizbullah masu karfi a kudancin kasar Lebanon.

Kakakin sojojin yahudawan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  ya yarda cewa an kashe sojojin wannan gwamnati 8 a wani artabu da mayakan kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon.

Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya ta kuma bayar da rahoton cewa, an kashe sojoji 8 na wannan gwamnatin a wani harin kwantan bauna da aka kai a cikin wani gini a kudancin kasar Lebanon.

Kakakin sojojin yahudawan sahyuniya ya sanar da cewa an kashe sojoji 8 tare da jikkata wasu 7, kuma yanayin wasu daga cikin sojojin da suka jikkata na da matukar muhimmanci.

Wadannan sojoji sun fito ne daga rukunin Golani da Ighuz.

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa, daga cikin wadanda suka mutu akwai jami'ai uku masu mukamin Manjo da jami'ai biyu masu mukamin kyaftin.

Wannan shi ne duk da cewa majiyoyin yaren Ibrananci sun sanar da adadin matattu fiye da haka.

Kafar yada labaran yahudawan sahyoniya Kan ta sanar da cewa sojojin wannan gwamnati suna fuskantar makiya masu taurin kai kuma gogaggu a kudancin kasar Lebanon.

An dauki lokaci mai tsawo ana kai dauki na kwashe matattu da kuma wadanda suka jikkata daga kudancin kasar Lebanon, domin kuwa dakarun da aka tura domin kwashe wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata sun fuskanci luguden wuta.

 

4240364

 

 

captcha