A rahoton tashar talabijin ta Al-Sumaria, sanarwar da aka buga a dandalin telegram na ofishin limamin Juma’a na birnin Najaf Ashraf, an kai hari kan gidan Hojjat al-Islam Sayyed Sadruddin Qubanchi, wanda wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai da sanyin safiyar yau 30 ga watan Nuwamba.
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hari gidan limamin da ke da ke unguwar al-Ghadir a Najaf Ashraf ta hanyar makaminj roka tare da gurneti, kuma an ce daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ya jikkata.