IQNA

Babban sakataren kungiyar Hizbullah:

Za mu ci gaba da bin tafarkin Shahid Sayyid Hassan Nasrallah

15:22 - October 31, 2024
Lambar Labari: 3492123
IQNA - Sabon babban sakataren Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya bayyana cewa, kungiyar za ta ci gaba da gwagwarmaya domin dakile makircin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin.

Sabon babban sakataren Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya bayyana cewa, kungiyar za ta ci gaba da gwagwarmaya domin dakile makircin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a kan daukacin yankin gabas ta tsakiya.

Sheikh Naim Qassem ya yi gargadin cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da masu goyon bayanta na yammacin Turai suna cikin wannan babban makirci da ake kitsawa yankin.

A  jawabinsa na farko da aka watsa ta gidajen  talabijin da dama a kasashen duniya a wannan Laraba, ya bayyana cewa, shirinsa na zahiri shi ne ci gaba da ayyukan marigayi Sayyid Hassan Nasrallah.

“Za mu ci gaba da aiwatar da shirin yaki wanda Sayyed Nasrallah ya tsara, kuma za mu ci gaba da kasancewa a kan turba ta siyasa daidai da manufofin kungiyar.”

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya jaddada cewa goyon bayan Gaza yana da matukar muhimmanci wajen tinkarar hatsarin  gwamnatin sahyoniya a yankin baki daya.

An kafa kungiyar Hizbullah ne a shekara ta 1982 domin tunkarar mamayar Isra’ila da manufar fadadarta da kuma ‘yantar da kasar Lebanon da ta mamaye, in ji Sheikh Qassem.

Ya kuma yi tsokaci kan sukar da ake yi cewa gwagwarmayar Gaza da Lebanon ne ya tunzura Isra’ila take aikata kisan kiyashin da take yi.

Ya ce : kada jama’a su manta da ta’asar da Isra’ila ta yi na tsawon shekaru 75, da kuma rawar da kungiyyoyin gwagwarmaya suka taka wajen kawo karshen mamayar haramtacciyar kasar kasar Labanon.

“Wasu suna yayata cewa an tsokani  Isra’ila, amma Isra’ila na bukatar hujja ne kafin ta aiwatar da ta’addanci? Shin mun manta shekaru 75 ana kashe Falasdinawa, da murkushe su, da kwace musu kasa, da kwace wurare masu tsarki da keta alfarmarsu da kuma  kisan kiyashi da Isra’ila ta yi a cikin tsawon wadannan shekaru? Shi ma an tsokane ta ne?

Gwagwarmaya c eta kori Isra’ila daga kasarmu, tare da hadin gwiwar sojoji da jama’ar kasa, amma  Kudirin majalisar dinkin duniya bai kori Isra’ila daga kasar Lebanon ba.” in ji sheikh Na’im Qassem.

 

4245342

 

 

 

 

 

 

captcha