IQNA

Daurin shekaru uku a gidan yari a kan wata mai fafutukar kare hakkokin Falasdinawa a Faransa

15:29 - November 07, 2024
Lambar Labari: 3492166
IQNA - An yankewa wata mai fafutuka da ke goyon bayan Falasdinu hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari da kuma tarar Yuro 13,500 bisa zargin tayar da hankali a Faransa.

A rahoton Al Jazeera, tsarin shari'a na Faransa ya yanke wa matar mai fafutuka da ke goyon bayan Falasdinu hukuncin daurin shekaru uku a gidan kaso, bisa zarginta da ta'addanci, saboda wallafa rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.

Wannan mai fafutuka ta goyi bayan Falasdinu ne a cikin rubuce-rubucenta tare da yin Allah wadai da kisan kiyashin da hHramtacciyar Kasar Isra'ila ke yi a zirin Gaza.

An yanke wannan hukunci a birnin Nice (Kudu maso Gabashin Faransa) a kan matar mai shekaru 34, wadda kotu ta yi ikirarin cewa ta same ta da aikata laifuka 13 da suka hada da cin zarafin bil'adama, tunzura wariya, yada kiyayya a kan yahudawa, da sauran tuhumce-tuhumce makamantan hakan.

Wannan mai fafutukar kare hakkokin  Falasdinawa tana daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar "From  Nice to Gaza" kuma tana daya daga cikin manyan jagororin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a Nice tun daga watan Oktoban 2013 da yahudawan sahyuniya suka kaddamar da yaki a kan al'ummar zirin Gaza.

Mai fafutukar goyon bayan Falasdinu ta ce a lokacin shari'ar da ake yi mata ba ta san illar da kalaman nata za su haifar ba.

Ta kuma ce a lokacin da take kare kanta: Ana ci gaba da gudanar da kisan kare dangi, an kashe mutane fiye da  40,000 sannan sama da mutane 100,000 sun  jikkata. Na yarda cewa na faɗi wadannan kalmomi, amma yarda da yadda a fassara su da cewa kalmomi ne na tayar da hankali da ta'addanci ba.

 

 

4246567

 

 

captcha