IQNA

Yarima mai jiran gado na Saudiyya a wajen taron OIC da kasashen Larabawa:

Muna Allah wadai da zaluncin da Isra'ila a kan Falastinu, Lebanon Labanon da Iran

15:13 - November 12, 2024
Lambar Labari: 3492192
IQNA -  Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya a yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kasa da kasa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi da Larabawa ya bayyana cewa: Kasarsa ta yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawan da take yi wa kasashen Labanon da Iran da Falastinu.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, shugabannin kasashe daban-daban sun gabatar da jawabai a wajen babban taron koli  na musamman na shugabannin kungiyar hadin kan musulmi ta OIC da kasashen larabawa da aka gudanar  a birnin Riyadh, inda suka yi Allah wadai da laifuffuka da cin zarafi na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Mohammed bin Salman, yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, a farkon taron na birnin Riyadh, ya bayyana cewa: Muna jaddada wajabcin ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar UNRWA, kuma ya kamata sauran kungiyoyin kasa da kasa su ci gaba da taimakawa Falasdinu.

Ya kara da cewa: Saudiyya na adawa da harin da Isra'ila ke kai wa kasar Lebanon, kuma wannan wuce gona da iri zai haifar da mummunan sakamako.

Ya ci gaba da cewa: Dole ne a yi Allah wadai da Isra'ila kan wuce gona da iri kan kasar Labanon, da kuma keta hurumin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Bin Salman ya jaddada cewa: Muna rokon Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin kawo karshen  wannan lamari , kuma muna jaddada cewa mamayar Falasdinu haramtaccen lamari ne.

A ci gaba da wannan taro, Mahmoud Abbas shugaban hukumar Palasdinawa shi ma ya bayyana cewa, kasashen duniya sun nuna gazawa ta yadda ba za su iya dakatar da wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawa suke yi a zirin Gaza ba.

Sarki Abdallah na biyu na kasar Jordan ya jaddada a taron da shugabannin kasashen musulmi da na larabawa  cewa: Kasashen duniya ba su yin abin da ya kamata wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen takawa Isra’ila burki dangane da kara ruruta wutar rikici da take yi Falasdinu da kuma kunna wata sabuwar wutar yaki a kasar Lebanon.

Ya kara da cewa: "Dole ne mu kara kaimi cikin gaggawa don kawar da shingen da aka sanyawa Gaza, da dakatar da tashin hankali a gabar yammacin kogin Jordan, da goyon bayan 'yancin kai na Lebanon da kuma dakatar da yakin da ake yi."

Ya nanata cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matsaya guda daya don hana afkuwar matsakar jin kai a zirin  Gaza da kuma cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take.

 

 

 

4247639

 

 

captcha