IQNA – A cikin manyan lambunan Shiraz na kasar Iran manoma da iyalai sun taru domin girbin rumman, alamar yalwa da rahamar Ubangiji.
Lokacin girbi yana farawa a watan Nuwamba kuma yana ɗaukar kusan watanni biyu. Yawancin girbin ana fitar da su ne zuwa kasashen yankin Gulf na Farisa, a cewar jami'an yankin.