IQNA

Harbe – harbe a ofishin jakadancin Isra'ila da ke Jordan

16:26 - November 24, 2024
Lambar Labari: 3492260
IQNA - Kafofin yada labaran gwamnatin Sahayoniya sun sanar a safiyar yau Lahadi cewa an harbe ofishin jakadancin Isra'ila da ke kasar Jordan, sannan 'yan sanda sun rufe yankin hanyoyin da ke kan ofishin jakadancin.

A cewar al-Arabi al-Jadeed, an ce wani mutum dauke da makamai ya bude wuta kan ofishin jakadancin Haramtacciyar Kasar Isra'ila da ke kasar Jordan a safiyar yau.

A halin da ake ciki, Hukumar Tsaron Jama'a ta Jordan ta ba da rahoton mutuwar wani mutum dauke da makamai a wata arangama da jami'an tsaro.

Wannan kungiya ta sanar da cewa jami'an tsaron Jordan 3 kuma sun jikkata a wannan rikici.

Wata majiyar tsaro ta kuma ce 'yan sanda sun bukaci mazauna garin da su zauna a gidajensu yayin da jami'an tsaro ke neman maharan.

Rahotannin da wadannan kafafen yada labarai suka fitar na cewa, jami'an tsaro sun tare hanyoyin da ke kan hanyar zuwa ofishin jakadancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke birnin Amman bayan an ji karar harbe-harbe.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar da cewa jami'an tsaro sun yi bincike a gidaje tare da kewaye ofishin jakadancin Isra'ila.

Ma'aikatan ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya sun bar kasar Jordan tun farkon yakin Gaza. An dauki wannan matakin ne bayan yakin da aka yi da Gaza kuma saboda fargabar gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin wannan gwamnati.

Yankin da ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya yake a ko da yaushe ya kasance wurin gudanar da gagarumar zanga-zanga a lokuta daban-daban.

 

 

 

 

captcha