IQNA

Tsaurara matakan Haramtacciyar kasar Isra'ila kan masu azumi a Masallacin Al-Aqsa

15:59 - February 25, 2025
Lambar Labari: 3492803
IQNA - Isra'ila na shirin takaita shiga harabar masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus, gabanin watan Ramadan mai alfarma.

Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar na shirin kara sanya takunkumi kan masu ibadar Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa a jajibirin watan Ramadan mai alfarma.

Takunkumin ya hada da tura ‘yan sanda 3,000 a shingayen binciken ababan hawa zuwa gabashin Kudus da Masallacin Al-Aqsa. Kahn ya kuma bayar da rahoton cewa, hukumomin Isra'ila za su hana Falasdinawa da aka sako kwanan nan shiga masallacin Al-Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na N12 na kasar Isra’ila ya bayyana cewa a cikin watan Ramadan, za a ba wa akalla mutane 10,000 damar shiga harabar masallacin Al-Aqsa domin yin sallar Juma’a, kuma shigarsu na da rajistar bukatar da kuma amincewar Isra’ila.

Kafafen yada labaran biyu sun ruwaito cewa mazan da suka haura shekaru 55 da mata sama da 50 ne kawai za a ba su izinin shiga masallacin, duk da cewa N12 ta ruwaito cewa yara ‘yan kasa da shekaru 12 kuma za a ba su damar shiga masallacin Al-Aqsa.

Galibi dubun dubatar Falasdinawa ne ke shiga harabar masallacin Al-Aqsa domin yin addu'o'i a cikin watan Ramadan.

Ban da haka, 'yan sandan Isra'ila ba za su bari Falasdinawa da aka sako yayin musayar fursunoni da ke da alaka da tsagaita bude wuta a Gaza su shiga masallacin Al-Aqsa ba.

Majiyoyin da ke magana da tashar talabijin ta N12 ta Isra'ila sun bayyana cewa halin da ake ciki a masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan ya dogara ne kan halin da ake ciki a Gaza.

 Jaridar Jerusalem Post ta nakalto majiyar tana cewa: Idan har aka tsagaita bude wuta, ana sa ran lamarin zai lafa, amma idan ba haka ba, za a jibge jami'an tsaro da yawa domin hana barkewar rikici.

Watan Ramadan mai alfarma da Masallacin Al-Aqsa na kara zama filaye a rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

 

4268217

 

 

captcha