A cewar Anadolu, Amy Pope, Darakta-Janar na Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM), ta rubuta a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na sirri ranar Laraba X, yayin da take ishara da abin da ta gani a ziyarar da ta yi a Gaza na baya-bayan nan: Al'ummar Falasdinu a Gaza ba su da wani zabi illa su kiyaye tsagaita bude wuta da tabbatar da tsaronsu.
Ta kara da cewa: Yawancin mutanen Gaza sun rasa komai, amma har yanzu suna da bege. Suna buƙatar wuri mai aminci da mutuncinsu da ƙoƙarinsu don makomarsu.
Gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da goyon bayan Amurka ta kaddamar da wani mummunan yaki a kan mazauna zirin Gaza daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2025, inda a cewar bayanan da aka samu, an kashe Palastinawa sama da dubu 160 da kuma jikkata a wannan yakin, wadanda galibinsu yara ne mata da yara. Sama da mutane 14,000 kuma an ba da rahoton bacewarsu a yakin.
Gwamnatin kasar ta kuma kai hare-hare da dama na sojoji a yankuna daban-daban na gabar yammacin kogin Jordan, inda suka raba dubun dubatar mazauna yankin.