A cewar jaridar Arabi 21, a ranar Juma’a 12 ga watan Afrilu hukumomin mamaye sun haramta wa Sheikh Muhammad Salim Muhammad Ali, mai wa’azin masallacin Al-Aqsa shiga wurin na tsawon mako guda, wanda zai iya tsawaita wa’adin.
Nan da nan bayan kammala hudubarsa da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa, inda ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan Haramtacciyar Kasar Isra'ila suke yi a zirin Gaza, an gayyaci Sheikh Muhammad Salim zuwa ofishin 'yan sanda na Al-Qishla da ke tsohon birnin Kudus domin gudanar da bincike cikin gaggawa.
A baya dai yahudawan sahyuniya sun yi irin wannan aiki, inda suka haramta wa Sheikh Ikrimah Sabri mai wa'azin masallacin Aqsa shiga wurin na tsawon lokuta daban-daban.