IQNA

Allah yayiwa fitaccen malamin kur'ani dan kasar Aljeriya rasuwa

16:37 - April 21, 2025
Lambar Labari: 3493129
Allah ya yi wa Sheikh Abdelhadi Laqab fitaccen malamin kur'ani dan kasar Aljeriya rasuwa a jiya Lahadi 11 ga watan Afrilu.

Shafin yada labarai na Al-Watan ya habarta cewa, Abdel Hadi Laqab ya kasance limamin jam’i kuma malamin kur’ani a kasar Aljeriya wanda ya bar ayyuka da dama a fannin karatu da tajwidi.

Ya karantar da Tajweed da karance-karance da tafsiri a tsangayar ilimin addinin musulunci ta jami'ar Algiers, kuma a shekarar 2019 ya samu digirin digirgir a fannin harshen larabci da kuma karatun kur'ani.

Sheikh AbdulHadi yana da lasisin karatun manya da kanana goma (karatun da aka danganta ga mashahuran malamai 10, wadanda suka fi yawa a tsakanin Ahlus Sunna) kuma ya halarci gasar kur'ani mai tsarki da dama a duniya.

Har ila yau, ya kasance mamba a kwamitin alkalan gasar kur'ani mai tsarki na kasa da kasa a kasashen Aljeriya, Saudi Arabia (King Abdulaziz Award), da UAE (Award Quran Dubai), kuma ya taka muhimmiyar rawa a cikin wadannan kwamitocin.

Abdul Hadi Laqab ya shahara da kokarinsa a fagen yada ilimin kur'ani da kuma kula da hanyoyin tadabburi a cikin kur'ani, kuma ya halarci taruka da dama na kasa da kasa da tarukan ilimi.

Wannan malamin kur'ani dan kasar Aljeriya ya bar kasidun kur'ani da bincike da dama wadanda suka yi tasiri a fagen ilimin kur'ani.

 

 

4277609

 

 

captcha