IQNA

Za'a daga Tutar Ghadir a Kasashe 42

19:10 - June 03, 2025
Lambar Labari: 3493357
IQNA - A daidai lokacin da Idin Al-Ghadir al-Khum ke karatowa Haramin Alawi ya tanadi tutocin Ghadir 75 da za a daga a kasashe 42 na duniya, baya ga lardunan kasar Iraki.

Da yake tsokaci a kan haramin Imam Ali Wissam Iskander shugaban cibiyar tsare-tsare da ci gaban haramin Alawi ya ce: Wadannan tutocin Ghadir sun bayyana irin amincin da al'ummar Iraki da kasashen duniya suke da shi ga Amirul Muminin (AS).

Ya ci gaba da cewa: A daidai lokacin da aka daga babbar tutar Ghadir a ranar 14 ga watan Zul-Hijja a hubbaren Imam Ali (AS) za a daga tutoci 22 a lardunan Iraki da sauran tutoci a kasashe 42 na duniya.

 

 

 

4286178

 

captcha