IQNA

Al-Ghamama; Masallacin Gajimare Da Ruwa

IQNA – Masallacin Al-Ghamama masallaci ne a Madina inda Manzon Allah (SAW) ya yi addu’ar neman ruwan sama.

Manzon Allah (SAW) ya yi addu’ar neman ruwa a wannan wuri a lokacin fari. Har yanzu bai gama sallarsa ba sai gajimare ya rufe shi kuma aka yi ruwan sama. Saboda haka, ana kiran wannan wuri Ghamama, ma'ana (girgije). Haka nan Manzon Allah ya jagoranci sallolin Idin Al-Fitr da na Idin Adha guda biyu a wannan masallaci.