IQNA

Yin bita kan hanyoyin shiga Intanet na masu ziyarar Arbaeen a ganawar da jami'an Iraqi da na Iran

16:04 - August 01, 2025
Lambar Labari: 3493641
IQNA - Ministan sadarwa na kasar Iraki kuma shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran ya yi nazari kan hanyoyin samar da hanyar intanet ga maziyarta  Arba'in a mashigin kan iyaka da kuma kan hanyoyin da ke kan hanyar zuwa birnin Karbala.

Ministan sadarwa na kasar Iraki, da shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran Pir-Hossein Kolivand, sun yi nazari kan tsarin samar da hanyar intanet ga mahajjatan Arbaeen a mashigar kan iyaka da kuma hanyoyin da suke kaiwa birnin Karbala mai alfarma.

Sanarwar da Ma'aikatar Sadarwa ta Iraki ta fitar ta bayyana cewa, an gudanar da taron ne tsakanin Al-Yasiri da Kolovand a ginin ma'aikatar sadarwa ta kasar Iraki bisa tsarin nazarin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, musamman wajen samar da ingantacciyar hidima ga masu ziyarar Arba'in na Imam Husaini (AS).

Sanarwar ta kara da cewa: A yayin ganawar an tattauna hanyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don samar da hanyoyin sadarwa da intanet kyauta a wuraren da mahajjatan Iran suke a kan iyakokin kasar da kuma tafiyarsu zuwa Karbala, ciki har da birnin Najaf Ashraf da kuma garuruwan Kazmin da Samarra masu tsarki, an kuma tattauna batun tallafawa ayarin motocin hidima a kan hanyar.

Sanarwar ta kuma ce, bangarorin biyu sun kuma tattauna batun bayar da tallafin fasaha na musamman ga lambar wayar tuntuba ta likitanci ta musamman da ke da alaka da kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Iran da ke cikin kasar Iraki don saukaka sadarwa kai tsaye da maziyarta da kuma samar da ayyukan jinya da kula da gaggawa ga marasa lafiya a lokacin aikin ziyara.

Al-Yasiri ya jaddada a cikin taron cewa ma'aikatar sadarwa ta shirya tsaf don yin amfani da dukkan karfinta na fasaha da dabaru da kuma kara kokarinta na tallafawa da kuma samun nasarar wannan babban taron addini.

 

4297462

 

 

captcha