Shafin sadarwa na yanar gizo na Mosaic FM cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da haddar hadisan ma’aiki a jiya Lahadi da safe 31 ga watan Agustan 2025 a Darul kur’ani da ke birnin Kairouan na kasar Tunisia. Wannan gasa tana gudana ne a karkashin kungiyar kasa da kasa da ke gudanar da maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Kairouan, tare da hadin gwiwar kungiyar kur’ani mai tsarki ta kasa.
Wannan gasa da ke zaman mafarin shagulgula da bukukuwan maulidin manzon Allah (s.a.w) ta kasa da kasa, ta samu halartar mahalarta daga lardin Kairou da daliban kur'ani na kungiyar kur'ani ta Kairou.
Daruruwan masu haddar kur’ani da masu sha’awar sunnar Annabi ne suka halarci wannan taron na addini. Wannan gasa ta ba da dama ga matasa su san juna da musayar abubuwan da suka faru da wasu.
Wannan taron na addini da na kimiyya shi ne aiki na farko a cikin tsarin bikin Maulidin Manzon Allah (SAW) na kasa da kasa a birnin Kairouan, wanda ya hada da jerin tarurrukan ilimi da laccoci na addini da ayyukan al'adu da ake gudanarwa sama da mako guda.
Da bude wannan gasa, birnin Kairouan ya shaida yadda aka fara gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (S.A.W) tare da tabbatar da matsayinsa na hedkwatar haske da ruhi da kuma wurin tarukan ilimi da addini da abubuwan tarihi na Musulunci.