IQNA

Baje kolin "Hadisai Arba'in" Da Aka Gudanar A Maulidin Manzon Allah (SAW) A Garin Herat

16:48 - September 05, 2025
Lambar Labari: 3493820
IQNA - A birnin Herat, daliban tsangayar koyar da fasahar kere-kere ta jami'ar Herat sun baje kolin ayyukansu a wurin baje kolin zane-zane na "Hadisai Arba'in" na maulidin Manzon Allah (SAW) da makon hadin kai.

A cewar jomhornews, wannan tarin zane-zane an tsara shi ne da tsarin koyarwar Manzon Allah (SAW) da kuma gabatar da bayyananniyar alaka tsakanin fasaha da ruhi.

Shugaban tsangayar Tawfiq Rahmani ya bayyana cewa makasudin gudanar da wannan baje kolin shi ne isar da sakonnin addini da na dabi’a ga al’umma ta hanyar fasaha.

Ya kara da cewa: Ta hanyar kirkiro ayyukansu na kirkire-kirkire, daliban sun yi kokarin isar da kyawawan hadisai da ruhi a cikin harshen fasaha.

A sa'i daya kuma, Hamidullah Ghiasi, shugaban kula da al'adu na sashen yada labarai da al'adu na kungiyar Taliban a birnin Herat, ya tunatar da goyon bayan cibiyoyin al'adu ga masu fasaha, musamman ma masu zane-zane, ya kuma jaddada cewa, wannan hadin gwiwa yana ci gaba da kasancewa a ko da yaushe.

A wani bangare na bikin, malaman addini da masana sun jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin musulmi da bin umarnin kur'ani da Sunnar Annabi. Baje kolin ''Hadisi Arba'in'' ba wai wata dama ce kawai ta baje kolin fasahar zanen daliban ba, har ma alama ce ta alaka tsakanin fasaha da ruhi da kuma hadin kan al'ummar musulmi na Herat.

 

 

 

4303414

 

 

captcha