IQNA

An kammala gasar kur'ani da hadisan Afrika a birnin Johannesburg

15:09 - September 23, 2025
Lambar Labari: 3493913
IQNA - Matakin karshe na gasar haddar Alkur'ani da Hadisan Manzon Allah "Sarki Salman bin Abdulaziz" na kasashen Afirka ya kawo karshen aikinsa yayin wani biki a birnin "Johannesburg" da ke kasar Afirka ta Kudu.

An  gudanar da bikin rufe gasar ne a yammacin jiya Asabar, tare da goyon bayan ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Saudiyya, da yada farfaganda da shiryarwa a cibiyar taro ta "Sanduto" dake birnin Johannesburg, kuma bikin ya samu halartar manyan jami'ai, jakadun kasashe, jami'an diflomasiyya da wakilan kungiyoyin addinin musulunci.

Kafofin yada labarai na cikin gida da na waje sun dauki nauyin bikin, kuma mahukuntan Saudiyya sun gabatar da jawabai tare da bayyana irin nasarorin da Saudiyya ta samu a kur’ani.

Sheikh Abdullatif bin Abdulaziz Al-Sheikh, ministan harkokin addinin musulunci, yada farfaganda da jagoranci na kasar Saudiyya, a jawabin da ya gabatar a wajen bikin, wanda mataimakin ministan harkokin addinin musulunci na kasar Awad bin Sabti Al-Anzi ya gabatar, ya ce kasar Saudiyya na gudanar da gasar haddar kur’ani ta kasa da kasa da na cikin gida, kuma ta kafa kungiyar buga kur’ani mai tsarki ta Sarki Fahd don tarjama kur’ani mai tsarki zuwa harsuna daban-daban.

Yayin da yake jaddada cewa kur'ani mai girma abin alfahari ne ga al'ummar musulmi, ya kuma yi kira ga mahalarta taron da su yi riko da kur'ani da aiki da koyarwar kur'ani da fahimtar ma'anonin sa daidai gwargwado, nesa da tsaurin ra'ayi da son zuciya.

Idan dai ba a manta ba a ranar Alhamis ne aka fara matakin karshe na gasar haddar kur’ani da hadisan ma’aiki a kasar Afirka ta Kudu, inda mahalarta 44 daga kasashe 29 na kudancin Afirka suka halarta.

Mutane 12 ne suka sami matsayi na farko a wannan gasa, tara daga cikinsu sun kasance a fagen haddar Alkur’ani baki daya, da surori goma, da surori biyar, sannan uku an gabatar da su a matsayin wadanda suka yi fice a fagen haddar Hadisin ma’aiki. Jimillar kyaututtukan da aka bayar na wannan gasa sun kai Riyal 300,000 na kasar Saudiyya, wadanda aka raba tsakanin wadanda suka yi fice a fagage daban-daban a wajen rufe gasar.

 

 

4306381

 

 

captcha