Majalisar dattawan musulmi karkashin jagorancin Ahmed Al-Tayeb Sheikh na Azhar, ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai a cocin Jesus Christ of Latter-day Saints da ke Grand Blanc a jihar Michigan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkata wasu da ba su ji ba ba su gani ba.
Majalisar dattawan musulmi ta jaddada tsayuwarta ta adawa da duk wani nau'i na tashin hankali da ta'addanci, wanda hakan ya sabawa koyarwar dukkanin addinai, dokokin Ubangiji, dokokin kasa da kasa da ka'idoji, da dabi'un dan Adam da kyawawan dabi'u wadanda suka haramta kai hare-hare a wuraren ibada da kuma kai hari kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Majalisar ta kuma yi kira da a karfafa kokarin kasa da kasa don inganta dabi'un hakuri da zaman tare cikin lumana.
Majalisar malaman musulmi ta bayyana cewa, tana jajantawa kasar Amurka da iyalan wadanda wannan danyen aikin ya rutsa da su, tare da yin addu'ar Allah Ta'ala da ya ba wadanda suka jikkata cikin gaggawa.
4308283