An gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ta dalibai ‘Gasar Al-Nour’ tare da halartar mahalarta daga jami’o’i 60 na Iran, Iraki, Tunusiya, Najeriya, Labanon, da ..., wadda jami’ar Al-Amid da ke birnin Karbala ta dauki nauyin shirya gasar.
Subhan Qari da Amir Hossein Allahvardi na jami'ar Tehran ne suka halarci wannan gasa, inda suka samu damar shiga matsayi na biyu a fannin bincike da haddar kur'ani mai tsarki.
Subhan Qari daya ne daga cikin masu gabatar da shirye-shiryen rediyon kur'ani.