IQNA

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Tir Da Allawadai Da Rusa Ofishin UNRWA Da Isra'ila Ta Yi A Quds

19:18 - January 22, 2026
Lambar Labari: 3494520
IQNA - Kungiyar Tarayyar Turai ta yi Allawadai dakakkausar murya kan rusa ofishin hukumar tallafawa Falastinawa ta MajalisarDinkin Duniya UNRWA a birnin Quds.

Tashar Aljazeera ta bayarda rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar Kungiyar Tarayyar Turai ta yi Allawadai dakakkausar murya kan rusa ofishin hukumar tallafawa Falastinawa ta MajalisarDinkin Duniya UNRWA a birnin Quds a cikin wannan mako.

Bayanin ya ce irin matakan da Isra'ila take dauka na yi hawan kawara kan dokokin kasada kasa abu ne da ba za a lamunta da shi ba.

Bayanin kungiyar ya ce UnRWA cibiya ce ta kasada kasada ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya,keta hurumin wannan cibiya keta hurumin dukkanin kasashen duniya ne.

Kungiyar ta gargadi Isra'ila da ta shiga cikin taitayinta,domin yin hakan zai jefa cikin karin wasu tuhume-tuhumen.

Sojojin yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan ofishin hukumar wanda yake birnin Quds sannan suka rusa shi da motocin boldoza a gaban mutane da 'yan jarida na kasa da kasa.

 

 

4329678

captcha