
Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Firayi Ministan Spain ya ce Kaddamar da harin Amurka da Isra'ila a kan Iran ya sabawa dukkanin dokokin duniya.
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalinsa na X ya bayyana cewa, yin gaban kai wajen kai hari kan wata kasa babu gaira babu sabar, yin hakan yana matsayinyin fatali da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Baya ga haka kuma ya ce kada Amurka ta kuskura ta yi amfani da sansanonin sojin kasarsa wajen kai wa kasar Iran hari.
Shi ma a nasa bangraen ministan harkokin wajen kasar ta Spain ya yi Allahawadai da hare-haren Amurka da Isra'ila a kan kasar Iran.
/4337920