
A yau ne aka fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki mai taken makarancin Tilmisan karo na shida a kasar Aljeriya.
Wanbnan gasa dai ana gudanar da ita da salo na karatun kur'ani ta tsohuwar hanya ta gargajiya, da nufin tabbatar da cewa wannan salo ya wanzu a raye.
Tun kimanin shekaru shida da suka gabata ne aka fara gudanar da wannan gasa a cikin watan ramadan mai alfarma kuma wannan gasa ta ci gaba da gudana da habaka.
Timisan na daya daga cikin tsoffin garuruwa na kasar Aljeriya wadanda suka shahara da ilimin kur'ani mai tsarki, kamar yadda kuma wanann birni ya suna wajen fitar da mayna malamai na addini a tarihi.
4338713