IQNA

Babban Sakataren Hizbullah

Ranar Quds Aalam ce Ta Kira Zuwa Ga 'Yantar Da Falastinu Da Kuma Nuna Kiyayya Da Zalunci

23:18 - March 13, 2026
Lambar Labari: 3494739
IQNA - Babban sakataren kungiyar Hib ullah a kasar Lebanon Sheikh Naeem Qassem ya bayyana cewa, ranar Quds ta duniya wata bababr alama ce ta motsi domin 'yantar da Falastinu daga zaluncin yahudawan sahyoniya.

A cikin jawabin da ya gabatar a yammacin yau, Babban sakataren kungiyar Hib ullah a kasar Lebanon Sheikh Naeem Qassem ya bayyana cewa, ranar Quds ta duniya wata bababr alama ce ta motsi domin 'yantar da Falastinu daga zaluncin yahudawan sahyoniya da suke mamaye da Falastinu.

Ya ce tabbas ranar kudus ta duniya a wanann shekara ta banbamta da sauran wadanda aka gudanar a shekarun baya, domin kuwa a wannan karon yahudawan sahyuniya sun kudiri aniyar kawo karshen duk wani yunkuri na 'yantar da Falastinu da Kudus daga mamayarsu.

Babban sakataren Hizbullah ya ce, Ranar kudus ta duniya na daga cikin muhimman abubuwan da Imam Khomeini ya gadarwa a l'ummar musulmi, wanda kuma a halin hikimar na ci gaba da kara bayyana ga kowa a duniya, kan cewa wannan yunkuri na 'yantar da dan adam daga bauta da mulkin mallaka da zalunci da danniya ta masu girman kai.

 

 

4340595

captcha