IQNA

Nazari Kan Yaki Da Sahyuniyanci A Cikin Kur'ani / 9

Daya Daga Cikin Manyan Jarabawoyi Shi Ne Tantancewa Tsaknain Gaskiya Da Karya

23:00 - March 17, 2026
Lambar Labari: 3494752
IQNA - Daya daga cikin mnyan jarabawoyi ga bayi ita ce iya tantance tsakanin gaskiya da kuma karya tare da bin tafarkin gaskiya komai wahala.

Kamar yadda wasu ayoyi suka yi nuni da da darussa masu muhimamnci a cikin rayuwa ta zamantakewa da imani da kuma akida, shi ne iya tantance tsakanin gaskiya da kuma karya tare da bin tafarkin gaskiya komai dacin hanyar.

Bayan yakin Uhud da kuma abubuwan da suka faru, da shidai da aka samu da kuma wadanda suka samu raunuka, ayata 137 a cikin suratu Ali Imran tana ishara da yadda aka bukaci muminai da su yi tadabburi da daukar darasi daga magabata, domin su ga yadda karshen wadanda suka karyata ayoyin Allah ya kasance.

Yakin Uhud yana daya daga cikin abubuwan buga misali a cikin tarihin musulunci, inda musulmi suka fuskanci jarabawa, amma kuma bisa hikima ta ubangiji da kyakkyawan jagoranci irin na manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka, musulmi sun yi amfani da hakan domin kara karfafa kansu da imaninsu.

Bayan nan Allah ya karfai muminai da cewa kada su samu rauni ko yin bakin ciki ko yanke kauna, matukar suna kan tafarkin gaskiya to kuwa tabbas su ne madaukaka indai har su muminai da gaske.

Sannan kuma Allah ya kara tausasa zukatansu da cewa, idan sun samu jarabawa a wanann yaki sun samu raunuka da kuma bayar da shahidai, to su ma kafirai sun samu irin wanann, sai dai bambancin shi ne su muminai a tafarkin gaskiya suke sabanin kafirai.

Allah ya kara da cewa wannan sunna ce daga cikin sunnoninsa, ya kan juya yanayi tsakanin mutane, wani lokaci a samu nasara wani lokaci kuma a samu jarabawa.

captcha