IQNA

Gangami A Gaban Fadar White House Domin Tunawa Da Yara 'Yan Makaranta Na Minab

23:11 - March 17, 2026
Lambar Labari: 3494753
IQNA - Amurkawa da dama ne suka taru a gaban fadar White House da ke birnin Washjngton na kasar Amurka, domin tunawa da yara 'yan mata 'yan makaranta na Minab da Amurka ta kashe.

Rahotanni daga shafukan sada zumunta na X sun habarta cewa, a yau Amurkawa da dama ne suka taru a gaban fadar White House da ke birnin Washjngton na kasar Amurka, domin tunawa da yara 'yan mata 'yan makaranta na Minab da Amurka ta kashe a ranar farko ta yakin da ta kaddamar kan Iran. 

Masu gangamin sun daga kwalaye da kyallaye da aka rubutua  klansu da ke yin Allawadai da wanann munan aiki na kisan kananan yara da Amurka ta yi a lokacin da suke cikin ajujuwan karatu.

Wannan lamari dai ya fuskanci kakakusar suka daga ko'ina cikin fadin duniya, tare da bayyana shi a matsayin laifin yaki, wanda ya cancancia  gurfanar da wadanda suka aikata hakan a gaban kuliya.

 

4341344

captcha