
a lokutan yanayin yaki ya sha banbam da na yanzu bisa la’akari da yadda duniya ta dunkule da kuma ci gaban da aka samu ta bangarori daban wanda yana da banbamci mai yawa da zamanin da.
Aya ta 120 a cikin suratu Tauba tana bayyana wannan matsayi ne na irin gudunmawar da kowa zai iya bayarwa a fagen daga, wanda hakan ya hada da abubuwa da yawa wadanda za a iya yi yanzu domin yaki da makiya Allah, wanda kuma yin duk wani abu a wanann fage wanda zai kawo cikas ga makircin makiya da suke domin cutar da addinin Allah da al’ummar musulmi shi am yana matsayin jihadi ne, kuma Allah zai bayar da lada kan hakan.
1 – Juriyar mutane kan wahalhalu a kan wannan tafarki da hakuri a kan rashi da yunwa da kishirwa.
2 – Mutane da suke taruwa a gangami ko jerin gwano domin nuna adawa da makircin makiya a kan addinin Allah suna da ladar jihadi.
3 – Wadanda suke a fagen daga suna gwabza yaki da makiya Allah domin akre addininsa da kuma al’ummar musulmi.
Dukkanin wadanda abubuwa ne wadanda suke nuni da irin gudunmawar da kowane mutum zai iya bayar wa wajen daukaka Kalmar Allah da kuma tunkarar makiya domin hana su cimma burinsu na cutar da addinin musulunci da kuma al’ummar musulmi, wanda kuma shi ne hakikanin abin da ayar take ishara das hi da kuima koyar da darasia kansa.
3496789
.