IQNA

Martanin Kungiyoyin Kur'ani Ga Makaranci Dan Kuwait Da Ke Goyon Bayan Trump Kan Kari A Kan Iran

23:09 - April 03, 2026
Lambar Labari: 3494793
IQNA - Kungiyoyin makaranta kur'ani mai tsarki sun ca a kan makaranci dan kasar Kuwait Rashid Al-afasi kan nuna cikakken goyon bayansa ga Amurka da Isra'ila kan harinsu a kan Iran.

A cikin bayanai daban-daban da suka fitar, Kungiyoyin makaranta kur'ani mai tsarki sun yi Allah wadai da kalaman Rashid Al-afasi makaranci dan kasar Kuwait  kan nuna cikakken goyon bayansa ga Amurka da Isra'ila kan harinsu a kan Iran.

Daga cikin bayananan da aka fitar har da yin kira ga makarancin da ya ji tsron Allah kan yadda ya yi watsi da abin da yake karantawa kulum a cikin kur'ani na ayoyin ubangiji.

Bayanin ya ce duk karantun da yake yi bai ga inda Allah ya ke jan hankalin musulumi da su guji karkata ga yahudawa ba, da kuma yadda aka bayyana cewa duk musulmin da ya jibinta lamarinsa gare su ya zama daya daga cikinsu.

Kamar yadda wata ayar ke fadi karara cewa yahudawa da nasara ba zasu taba yarda da musulmi har sai idan ya bi tafarkinsu.

Makarancin dai ya bayyana goyon bayansa tare da yin kira ga Trump da ya mayar da Iran wurin luguden wuta babu kakkautawa, yana yin wannan kiran ne bisa ga dalilai na akida da kuma alakr gwamnatinsa da yahudawa.
 
/4344074

captcha