
Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, sakamakon shan kakkausar suka daga ko'ina a cikin fadin duniya kan saka hoton cin zarafi ga Annabi Isa (AS) shugaban kasar Amurka Donald Trump ya goge hoton daga shafinsa.
Trump kamar yadda ya saba a cikin izgili ya sheda wa manema labarai cewa, shi ne ya saka hoton da kansa, yana sanye da fararen kaya kamar Yesu Almasihu, yana raba haske ga marasa lafiya.
Ya ce shi ne da kansa domin aikinsa kenan taimaka ma mutane da basu taimako domin su rayu, saboda haka bai ga wani abin magana ba domin ya kwatanta kansa da Annabi Isa.
Bayan saka wannan hoto jagoran kiristoci mabiya darikar katolika Paparoma Leo na 14 ya kakkausar suka a kan hakan, tare da bayyana siyasar gwamnatin Trump da cewa siyasa ce mara kyau, wadda ba take keta alfarmar abubuwa masu daraja.
Trump ya ce ba zai nemi wata afuwa daga Paparoma, domin a cewarsa Paparoma ya yi maganganu na shirme a kan gwamnatinsa.
4346332