IQNA

Kimanin Masu Ziyara Dubu Goma Ne A Rana Ke Ziyartar Karbala'a

Bangaren manema labarai: Jalal Bitarafan ya bayyana cewa; mai kula da guraren ziyara a hukumar kula da hajji ya bada labarin cewa; kumanin masu ziyara dubu koma n eke ziyartar Karbala'a a kowa ce rana.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: hukumar kula da hajji da umara a iran ta bayyana cewa nan bad a jimawa ba za a samu Karin masu son ziyartar hubarin Imam Huseini (AS) da ke karbala zuwa Karin dubu hudu. Huseini Akbari mai kula da bangaren ziyara a hukumar ya kara da cewa: watanni biyu da suka gabata an samu Karin masu ziyartar wannan guri na ibada da kusan dubu uku kuma bayan tuntubar mahukumtan Iraki mun amince tare da su da yin hassashen Karin adadin da za su iya tafiya wannan kasa kuma babban dalili takaita yawan masu bukatar ziyartar wannan gurin na Ibada shi ne karamcin abubuwan da maziyatar ke bukata a Iraki amma yanzu za su iya kai yawansu kimanin dubu goma.

367095