IQNA

Ayatullahi Kablan Ya Bukaci ya Katolika Su Hada Kai Da Palasdinawa

12:38 - October 26, 2010
Lambar Labari: 2020062
Bangaren siyasa da zamantakewa; Ayatullahi Abdallah Amir Kablan mataimakin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi';a a kasar Labanon bayan ya yi nuni da muhimmancin hada kai da nuna yan uwantaka tsakanin kirsitocin katolika da al'ummar Palsdinu ya bukaci a taron komitin yan katolika na yankin gabas ta tsakiya a Kudus da su yi aiki da hakan.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshen kamfanin da ke kasar Labanon ya watsa rahoton cewa; Ayatullahi Abdallah Amir Kablan mataimakin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi';a a kasar Labanon bayan ya yi nuni da muhimmancin hada kai da nuna yan uwantaka tsakanin kirsitocin katolika da al'ummar Palsdinu ya bukaci a taron komitin yan katolika na yankin gabas ta tsakiya a Kudus da su yi aiki da hakan.Wannan kira da bukata ta shi tana da matukar muhimmanci musamman idan aka yi la'akari da alfanon da ke tattare a cikin hakan da kuma yadda hada kai tsakanin al'ummar palsdinu da kiristocin Katolika zai taimaka ainin wajen samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.



682253
captcha