IQNA

Ali Fadlullahi Ya Jaddada Wajibcin Dangantaka A Tsakanin Jagororin musulmi

10:48 - October 27, 2010
Lambar Labari: 2020641
Bangaren siyasa zamantakewa: Said Ali Fadllullahi shugaban muassisar Allama Fadllullah a kasar labanon a lokacin day a ke gabatar da wani jawabi ne ya jaddada wajibcin samar da wata hanya ta tuntuba da danganta a tsakanin shugabannin musulmi a aikace.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshen kamfanin da ke kasa labanon ne ya watsa rahoton cewa; Said Ali Fadllullahi shugaban muassisar Allama Fadllullah a kasar labanon a lokacin day a ke gabatar da wani jawabi ne ya jaddada wajibcin samar da wata hanya ta tuntuba da danganta a tsakanin shugabannin musulmi a aikace. Sai Ali Fadllulah ya fadi haka ne a lokacin day a ke gabatar da hudubar sallar juma'a ya yi wannan kira da ke a wani matsayi na jan kune da fadakarwa kan irin muhimmanci da ke tattare na shugabanni da jagororin musulmi su hada kansu domin sanin yadda za su samu ilimi da masaniyar halin da mutanan su suke ciki da kuma tunanin hanyoyin da za su bi domin magance masu matsalolinsu da tunkarar makiyansu.


682787

captcha