IQNA

Wani Rahoto Ya Tabbatar Da Yaduwar Musulunci Cikin Sauri A Amurka

15:44 - February 13, 2011
Lambar Labari: 2080271
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar da ke gudanar da bincike kan yadda addinai ke samun karbuwa a tsakanin al'ummomin kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa yanzu addinin Musulunci na samun karbuwa fiye da sauran lokutan baya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lefigaro an bayyana cewa, wata cibiyar da ke gudanar da bincike kan yadda addinai ke samun karbuwa a tsakanin al'ummomin kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa yanzu addinin Musulunci na samun karbuwa fiye da sauran lokutan baya a kasar, musamman ma a cikin shekarun baya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan rahoto ya tabbatar da yadda sukar addinin Musulunci da nuna kyamarsa da wasu daga cikin masu tsatsauran ra'ayin gaba da Musulunci suke yi, ya kara ma addinin muslunci farin jinni da kuma karbuwa tsakanin al'ummar kasar Amurka.

Wata cibiyar da ke gudanar da bincike kan yadda addinai ke samun karbuwa a tsakanin al'ummomin kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa yanzu addinin Musulunci na samun karbuwa fiye da sauran lokutan baya a kasar ta Amurka.

744562





captcha