IQNA

Yan Sandan Saudiyya Sun Kai Hari Kan Misrawa Masu Ziyara

18:53 - September 04, 2011
Lambar Labari: 2181214
Bangaren kasa da kasa, rahotanni sun yi nuni da cewa 'yan sandan kasar saudiyya sun kai hari kan mutanen kasar Masar da suka je aikin Umra a babban filin safka da tashin jiragen sama na Jidda.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya samu an sheda cewar 'yan sandan kasar saudiyya sun kai hari kan mutanen kasar Masar da suka je aikin Umra a babban filin safka da tashin jiragen sama na Jidda wanda shi ne babban filin jirgin sama na kasa da kasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa gwamnatin kasar saudiyya tana daukar matakai na takura masu zuwa gudanar da ayyukan umra da hajji daga kasashen musulmi, kuma ana ganin cewa daukar wannan mataki akan mutanen masar ba zai rasa nasaba da kawar da babban aminin Saudiyya da suka daga kan mulkin kasarsu ba.

'Yan sandan kasar saudiyya sun kai hari kan mutanen kasar Masar da suka je aikin Umra a babban filin safka da tashin jiragen sama da aka edaukar alhazai a jidda, lamarin day a bakanta ran dubban masu gudanar da ayyuakn ibada.

853388



captcha