IQNA

Za A Fara Gudanar Da Zaman taro na Cibiyoyin Ilimin Addinin Muslunci A Faransa

14:43 - November 26, 2011
Lambar Labari: 2229098
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da wani zaman taro na cibiyoyin ilimi da yada al’adun addinin muslunci a kasar faransa tare da halartar masana daga jami’oi wanda zai gudana a birnin Paris.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na elmedina cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro na cibiyoyin ilimi da yada al’adun addinin muslunci a kasar faransa tare da halartar masana daga jami’oi wanda zai gudana a birnin Paris fadar mulkin kasar daga yau Asabar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka yanzu haka babbar cibiyar kula da harkokin muslunci ta kammala dukkanin shirye-shiyen wannan taro, wanda za a gabatar da laccoci kan mahangar muslunci dangane da matsayin ilimi da kuma al’adu, da irin rawar da suke takawa wajen ci gaban kowace al’umma.
Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai akwa masana musulmi daga kasashen yankin gabas ta tsakiya, wadanda su ne za su bayyana mahangar muslunci kan wannan maudu’i, hak anan kuma su ma masana dag akasar za su bayyan abain da suka fahimta kan haka.
Fara gudanar da wani zaman taro na cibiyoyin ilimi da yada al’adun addinin muslunci a kasar faransa tare da halartar masana daga jami’oi wanda zai gudana a birnin Paris, hakan na da matukar muhimmanci ga musulmin kasar.
904859

captcha