IQNA

An Samu Karuwar Maharlata Olympik Na Kur'ani A Baku

15:07 - July 01, 2012
Lambar Labari: 2358371
Bangaren harkokin kur'ani mai girma:a gasar kur'ani da aka yi wa lakabin Olumpik na Kur'ani a jamhuriyar Azarbaijan da wakilin hukumar da ke kula da harkokin al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Baku ya shirya an samu karuwar mahalarta wannan gasar da kaso shidda idan aka kwatamta da shekarar da ta gabata ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shamsiya da ta gabata.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a gasar kur'ani da aka yi wa lakabin Olumpik na Kur'ani a jamhuriyar Azarbaijan da wakilin hukumar da ke kula da harkokin al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Baku ya shirya an samu karuwar mahalarta wannan gasar da kaso shidda idan aka kwatamta da shekarar da ta gabata ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shamsiya da ta gabata. Ibrahim Nuri mai kula da harkokin al'adu na jamhuriyar musulunci ta Iran a wata tattaunawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Kur'ani Ikna a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa:a wannan karo an samu halarta wannan gasar kur'ani ta Olumpik na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya am samu halartar mutane dari biyu da hakan yake nuni an samu karuwar mahalarta da suka rubinya har sau shida da kuma hakan ke nuni a fili da yadda mutane suka karbi wannan gasar da kuma tabbacin cewa wannan gasar tana da muhimmancin gaske a gare su .
1040585
captcha