IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar karatu Da Hardar Kur’ani A Kasar Tunisia

21:58 - September 02, 2012
Lambar Labari: 2403593
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia tare da halartar wakilan cibiyoyin addinin musuluncimusamman na kur’ani daga sasa na kasar inda za a tantace wadanda za su kai matakin karshe.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AZD, cewa yanzu haka dai an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia tare da halartar wakilan cibiyoyin addinin musuluncimusamman na kur’ani daga sasa na kasar inda za a tantace wadanda za su kai matakin karshe tare da ba su kyautuka.
Shi kuwa Mansur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi kamar yadda ake gani a duk inda suka wata kungiya ko cibiya, a cikin kasashen musulmi da ma kasashen da ba na musulmi ba.
Ya ci gaba da cewa dle ne a dauki dukaknin matakan da suka dace domin takawa ‘yan salafiyya burki kan ayyukansu na wuce gona da iri, tare da kara fadakar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaurace ma su neman fitina acikin al’ummar musulmi, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai kawo zaman lafiya a cikin al’umma.
Masur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi, domin kawai su cimma manufofinsu, ko kuma zatra da manufofin wasu bisa sani ko bisa jahilci.
1089358






















captcha