IQNA

An Bude Wurin Horar Da Malaman Kur’ani A Karbala

23:28 - March 19, 2016
Lambar Labari: 3480244
Bangaren kasa da kasa, Darul kur’an na hubbaren Hussaini ya bude wata cibiya domin koyar da malaman kur’ani da kuma ba su horo a Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafin hubbaren Imam Hussain cewa, an bude wannan cibiya ne ta bayar da horo ga malaman kur’ani, bisa la’akari da bukatar hakan.

Hojjatol Islam Mansuri shi ne shugaban wannan shiri, ya kuma bayyana cewa shirin zai kunshi bangarori daban-daban, inda malamai masu digiri kan ilmomin kur’ani za su samu horo na koyar da yara a makarantu kan ilmin kur’ani mai tsarki.

Ya kara da cewa an samar da dukkanin abubuwan da akebukata domin tabbatar da cewa wannn shiori ya yi nasar akamar yadda aka tsara shi, domin kuwa za a dauki malaman da za su samu horon ne daga dukaknin bangarori na al’ummar kasar Iraki, kamar yadda kuma dukkanin al’ummar kasar ne za su ci gajiyar shirin da yardarm Allah madaukakin sarki.

3484191

captcha