IQNA

Fara Aikin Tarjamar Kur’ani A Cikin Harsuna 6 A Hadaddiyar Daular Larabawa

17:38 - March 30, 2016
Lambar Labari: 3480274
Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada al’adun muslunci ta Zayid a hadaddiar daular larabawa ta fara gudanar da wani shiri na tarjamar kur’ani a cikin harsuna 6.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albayan cewa, babbar cibiyar nan ta yada al’adun muslunci ta Zayid a hadaddiar daular larabawa ta fara gudanar da wani shiri na tarjamar kur’ani a cikin harsuna 6 su ne, Faransanci, China, Philipines, Indonesia, Urdu, da Spanish.

Wannan cibiya ce za ta dauyin aiwatar da wanann shiri da nufin kara yada koyarwar kur’ani da fahimtar da wasu ma’anoninsa da abin da ya kunsa.

Nidal Tunaiji shi ne babban darakta na wannan cibiya, ya kuma bayyana cewa wannan yana daga cikin shirinsu na shekara ta 2016 zuwa 2020.

Ya kara da cewa babbar manufarsu ta gudanar da wananns hiri ita ce, sun fahimci cewa yada karantawar kur’ani zai taimaka muatuka wajen ilmantar da musulmi da bas u jin larabci, kamar yadda kuma zai taimaka wajen yada shi ga mutane da ba musulmi da suke san sain abin da ke, domin su gane cewa kur’ani littafi mai koyar da kyawawan dabiu na zamantakewa.

3484924

captcha