IQNA

Wata Sabuwar Muslunta A Amurka:

Kamalan Kin Muslucni Da Trump Ke Ya Sani Bincike A Cikin Kur'ani

22:41 - November 14, 2016
Lambar Labari: 3480940
Bangaren kasa da kasa, wata mata ba'amurka mai suna Liza Shanklin ta sanar da karbar addinin muslunci sakamakon yin bincike a cikin kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, matar mai suna Liza Shanklin ta bayyana cewa, sakamakon yadda Donald Trump ya rika sukar addinin muslucni a lokacin yakin neman zabensa, hakan ya zaburar da ita wajen karanta kur'ani domin ta ga abin da ke cikinsa, dalilin hakan kuma ta karbi addinin muslunci.

Matar ta ci gaba da cewa, sau da yawa idan ana Magana kan wani abu takan so ta duba abin domin tabbatar da gaskiya ko akasin hakan kana bin da ake fada.

Kuma wannan shi ne bababn abin da ya sanya ta yin kokarin ganin ta nemi kwafin kur'ani mai tsarki domin ganin abin da ke ciki, wanda ake sukar musulmi a kansa, kuma bayan ta karanta sai ta samu natsuwa da dukanin abin da ke ciki, tare da yin imanin cewa hakika wannan littafi ba daga dan adam yake ba.

Daga karshe dai ta yanke shawar karbar addinin muslucni, inda a ranar da aka sanar da cewa Trump ya ci zabe, ta shekata a fhafinta na facebook kan cewa ta karbi addinin muslucni, bayan gamsuwa da cewa hakiak wannan addini daga Allah yake.

Ta ci gaba da cewa a halin yanzu tana saka hijabi, amma har yanzu ba ta sanar da hakan ba a bayyane, amma ranar 20 ga watan Janairun 2017, za ta shelanta cewa daga ranar za ta ci gaba da saka hijibi har karshen rayuwarta, kuma za ta shiga da shi koina cikin kasar Amurka ba tare da wani fargaba ba.

3546028


captcha