IQNA

Sarkin Morocco Ya Kira Kansa Amirul Muminin

23:51 - November 27, 2016
Lambar Labari: 3480979
Bangaren kasa da kasa, sarkin kasar Morocco Muhammad na 6 ya kira kansa Amirul muminin a lokacin da yake gudanr da ziyara a Madagaskar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar alalam cewa, a lokacin da sarkin Morocco yak e gudanar da ziyara tare da amsa tambayoyin manema labarai ya bayyana cewa, abin da wasu ke yadawa dangane da wani shiri da kasar Morocco take da shin a mamaye lamurran kasashen musulmi babu gaskiya a cikinsa.

Sarkin ya ce kasar Morocco a matsayinta na babbar kasa daga cikin kasasashen msuulmi kuma shi a matsayinsa na sarkin wannan kasa yana matsayin Amirul muminin na dukkanin musulmi.

Ya kara da cewa za su gigaba da gudanar da dukkanin shirye-shirye na taimaka ma kasashen musulmi ta fskar ilmantarwa da kuma nuna musu hanyar manzon Allah.

Bisa koyarwar ahlul bait bab wani mutum da ake kira da lakabin Amirul muminin sai Imam Ali (AS) domin shi kadai manzon Allah ya kira shi da wannan lakabi.

3549224


captcha