Bugu da kari, Ibrahim Musa ya bukaci ganin shugaban kasar ta Najeriya ya sa an binciki kisan da aka yi wa mambobin harkar ta musulunci.
Kamar yadda kuma ya bayyana cewa a kowane llokaci suna gudanar da lamurransu lami lafiya, ba tare da wani abu ya taba faruwa ba, amma idan jami'an tsaro suka afka musu sai a bayyana hakan da cewa su ne suka tayar da hankali.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da dama sun bukaci gwamnatin ta Najeriya da ta saki sheikh Ibrahim Zakzaky ba tare da wani bat alokaci ba, amma dai har yanzu ana ci gaba da tsare a wani wuri da ba a sani ba, bayan dauke shi daga wurin da jami'an tsaron farin kaya suka yi a baya a wani wuri a birnin Abuja.
Daruruwan mutane ne dai sojojin kasar su ka kashe a harin da su ka kai a Husaniyar Bakiyyatullah a 2015 da kuma gidan Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky.