IQNA

Al’ummar Bahrain Na Jan Kunnen Masarautar Kasar Lafiyar Ayatollah Isa Kasim

20:46 - December 02, 2017
Lambar Labari: 3482160
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga kasar Bahrain sun bayyana cewar al'ummar kasar sun gudanar da wasu sabbin zanga-zangogin kin jinin mahukuntar kasar da kuma bakar siyasar da suke gudanarwa musamman ci gaba da killace babban malamin Shi'a na kasar Sheikh Isa Qassim da gwamnatin take yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Rahotannin sun ce an gudanar da zanga-zangogin ne a garuruwa daban-daban na kasar da suka hada da garin Sanabis da ke wajen birnin Manama, babban birnin kasar ta Bahrain bugu da kari kan yankin Abu Sabi da lardin Maqsha da ke kusa da kauyen Diraz, da dai sauran garuruwa na daban.

Jami'an tsaro dai sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar musamman a garuruwan Diraz da Abu Sabi din inda suka kama wasu mutane da ci gaba da tsare su.

Masu zanga-zangar dai sun fito ne don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da killacewa da kuma daurin talalan da jami'an tsaron kasar ta Bahrain su ke wa Sheikh Isa Qassim din sama da kwanaki dari biyar din da suka gabata bayan da gwamnatin kasar ta kwace masa takardar zama dan kasa da kuma kokarin da suke yi na korarsa daga kasar.

3668711


captcha